SIRRIN GANYAN ZOGALE (MORINGA)
AMFANIN ZOGALE GA DAN "ADAM (MORINGA) 1. Ana dafah ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulser) 2. Ana shafa danyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai. 3. Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe yaji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogalen insha Allah jinin zai tsaya. 4. Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa. 5. Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa. 6. Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari. 7. Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa 'yar kadan domin maganin ciwon shawara. 8. Ga mai fama da ciwon ido zai dinga diga ruwan danyen zo gale haka ma mai fama da ciwon kunne. 9. Macen dake shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono. 10. Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar diabetes ya rinka shan furan zogale da citta kamar shayi. 11. Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi...
Comments
Post a Comment