SIRRIN GANYAN ZOGALE (MORINGA)
AMFANIN ZOGALE GA DAN "ADAM (MORINGA)
1. Ana dafah ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulser)
2. Ana shafa danyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.
3. Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe yaji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogalen insha Allah jinin zai tsaya.
4. Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.
5. Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa.
6. Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.
7. Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa 'yar kadan domin maganin ciwon shawara.
8. Ga mai fama da ciwon ido zai dinga diga ruwan danyen zo gale haka ma mai fama da ciwon kunne.
9. Macen dake shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.
10. Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar diabetes ya rinka shan furan zogale da citta kamar shayi.
11. Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi.
12. Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga Yara.
13. Ana daka ganyen zogale da 'ya'yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.
14. Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya 'ya'yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.
15. A daka zangarniyar zogale da 'ya'yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karfin da namiji da sa maza kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.
16. A daka saewar zogale da 'ya'yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (appendix).
17. Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon AIDS zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale .
18. Haka kuma mai fama da typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawaraa, zai iya yawaita shan ruwaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.
ππ»domin samun bayanae akan 'ya'yan itatuwa kubiyo mu 'aππ»
Telegram:t.me/novelchamber
mrnovelbooks.wordpress.com
mrnovel2.blogspot.com
Comments
Post a Comment