NIDA DALIBATA CMPLT PART 2

πŸ…Ώ11&12

Azuciye yake bin bayan Fatima ,azuciyarsa kuwa cewa yake lallai yarannan  basu sanniba amma zakugane kuranku.

Dede nan suka iso gun ,tunkafin ya ida isowa ,atsawace yace ma duka Pripet  din, suyi kneeling.

Hafsat na ganin sa tayi murmushi ,takara fitowa yadda zai ganta.

Kallon sa yamayar gun SS2 ,nanko yahangota ,cikin isah yakutsa kai ,

Cikin layin datake ,afusace ya finciki hannunta ,yafito da ita, suka karya kwana ,

Sannan yacikata hade da Jan tsaki, yace matsoraciya kawai, keda Bakida lfy me yasa kkaje  compound?

Sunku yadda kanta tayi tace sir inbanjeba dukana fa zasuyi ,shiyasa naje.

Hararar ta yyi yace to sarkin tsoron duka ,aisuma yanzun jikin nasu zegaya masu.

Marairai cewa tayi tace sir pls kada kayi musu komai ,wlh guna zasu rama.

Tsaki yyi yace su kasheki insun tashi ,oya kije ga key din office dina kije kijirani.

Hawaye tafara pls sir kada kasa adakesu kaji...

Kallon ta yyi yace ,Hafsat yaushe nafara wasa dake ne wai ,wurgama key din yyi yace kigoge hawayen nan.

Mak'e kafad'a tayi ,alamar ah ah , yi yyi kamar xedaketa Aiko ta gudu tana dariya.

Shima murmushi yyi,yadauko wayarsa yakira mlm rabe yace yazo yanzun yasamesa a hostel ,Kuma yazo bulala.

Yana kashewa ,yanufi gunda yasasu kneeling.

6angaren Pripet kuwa, sir Aliyu na tafiya shida Hafsat,

Labour tace wlh yajamata dan sai nayi mata shegen duka wlh.

Takusa da,ita ,tace hmm ai inde kan wannan yarinyar ne ze iya yin komai , dan kwanaki dana kashe mata bucket ,bakiga rashin mutumcin da yyimunba.

Wata  tace to kodai Santa yake ne, wata tace ke ah ah wannan dan jin kan ze iya furta yanason dalibarsa.

K'anwarsace, ai shiyasa yake Wannan hura hancin akanta ,bakuga ba har kama suke .

Wata tace eh wlh kuwa,Aiko xata gane shayi ruwane ,tunda sbd ita yasa mu kneeling gaban yara muna Pripet.

Dede nan sir Aliyu yakaraso,kallon gyama yabisu dashi kamar yaga kashi.

Adakile yace  ,zaku gane bakuda wayo , dan ni bakuda K'imar da zan dakeku da  hannuna zansa azanemunku.

  Ana haka , mlm rabe ya iso da bulalarsa ,Yana girgizata ,tasha mai ,dama abinda yakeso kenan.

Kallon sa  sir Aliyu yyi yace mlm sunmin  laifi inaso jikinsu yagayamusu.

Murmushi mugunta mlm rabe yyi yace angama ranka yadade.

Nan mlm rabe yacigaba da jibgarsu,sir Aliyu yyi tafiyarsa.


Straight office insa yanufa ,Aiko yasami Hafsat ta gyara office in sai kamshin room freeshner yake.

Murmushi yyi yaji Dadi har cikin ransa.

Amma azahiri saiya kalleta ,yace kewayasa  ki gyaramun office nasakine. 

Ahankali tace sir yi hakuri ,ba Wanda yasani.

Hararanta yyi ,ya shige bed room yadawo da magani a hannunsa yabata.

Ta karba ,wasu swan yabata yace tasha maganin,kallon sa tayi tace zansha a class.

Bece mata komaiba, yasake mik'a mata ,zatasake magana ,taga ya aje swan din fuskarsa adaure,

Yace  get out of my office, tayi mugun tsorata ,taso basa hakuri amma saiyashige bed room ya buga k'ofar da karfi.

Haka ta tafi class ba walwala ,duk sai taji ba Dadi.

Azuciyarta kuwa ca take anya kinyi  adalci kuwa, miyasa baki karba ,duk irin kok'orin dayake akanki.

Kinsan bbu yarinyar data isa yakulata saike, yake kulawa wasu na zaton ke kanwarsace ,shine kika bata masa rai.

Haka ,Hafsat tayini sukuku,har Fatima ta lura da ita ,ta tambayeta,lfy ,sai tace ba komai.

 Bayan antashi dg class, ankarbi  abincin rana ,su Hafsat na zaune akwanarsu ,itada fatima.

Alokacin har sunyi wanka,kawai saiga wata Pripet tashigo ,

Ta watsawa Hafsat mugun Kallo ,tace ke biyoni,ta juya.

Jikin Hafsat se rawa yake tabita abaya dama tason xa arina.

Fatima na ganin haka ,ahankali itama tabisu ta labe taga gugun dasuke zaune ga bulali nan na bedi agabansu sunsa Hafsat kneeling.

Suna cewa ,hmmm yarinya yau sai kin gwammace dama bakixo duniyarba.

Ai Fatima najin haka da gudu ,tayi hanyar area class.

Dan takira sir Aliyu, duk da tana tunanin qila bayanan,tunda in antashi class becika zama askul inba duk da nan yake kwana.

Tana isowa tasamesa Yana rufe office ,yasha wankan farar shadda sai kamshi yake.

Cikin nishi hade da shashsheka ,Fatima ke cewa sir sir sir!!!

Saurin kallonta yyi yace ke lfy meke faruwa?

Da sauri ta ce Hafsat  na gun Pripet wlh zasuyi mata duka su dukan su ,da bulalai na bedi,

Arazane yace da gaske kke ,tace eh wlhy, muje kawai yace ,cikin sauri yake tafiya .

Harda gudu Fatima tahada ganin xewuceta .

Shikuwa ransa yabaci matuka ,yakagara su iso idanunsa sunyi jajir .

Alamun ran yan maza yabaci, kamar wani xaki haka yake huci ,Yana fesar da iska me zafi abakinsa.

6angaren su Hafsat kuwa ,ciremata hijab sukayi sai kuka take tana basu hakuri ,amma basu saurareta suna hau jibgarta.

Kota ina kuka take har  oya karfinta ,sunmata rubdugu ,sun fashe mata jiki abinka da farar fata duk jikinta yyi ja ga shatin bulalar rad'o rad'o ajikinta.


Labour ce datafi kowa tsanar Hafsat ,ta d'auko almashi ,ta nacewa,

yau zandatse gashin datake takama dashi ta cire mata  dankwali.

Taso ta hana amma bata ,iyawa sbd ta jigatu ahannunsu,

Tana gani ta d'aga almashi ta saita  gashin da nufin datsewa.

Hafsat kuwa runtse idanunta tayi,dan tarigada tasadakat zasu datsemata gashi.

Kamar amafarki ,taji muryar sir Aliyu nace wa kika datse mata gashi wlh sai kinyi nadamar dabaki tabayiba arayuwarki.

Da sauri ta bud'e idonta tagansa kamar wani xaki, da gudu ta tashi ta fada ajikinsa tasaki kuka.

Wani irin tausayinta yaji ,ahankali yadago kanta yasa yatsansa ,yashare mata hawaye.

Sannan yakalli Fatima dake gefensa yajanye Hafsat dg jikinsa yace kamata kuje daki.

Ba musu Fatima ta kamata suka wuce daki,

Azuciye yyi gun labor ,yyi mata wani wawan mari mai rai da lafy,yasake mata wani.

Atake tasaki alma kashin hannunta  sbd wasu stars da tagani suna mata shawagi a ido.

Saida jinta na wucin gadi yadauke ,atake yatsunsa suka kwanta afuskarta.

Afusace yabar gurin ,yyi step quarters.

gidan PC yaje yasanar da ita tun dg sadda yasa akirata da safe har xuwa yanzun.

Ran PC yabaci ,nan takira vice dinta da Mlm rabe ,suka rankaya a hostel.

Har daki sukaje  taga yadda suka mata irin wannan duka kamar jakarsu.

Nan suka isa gun da Mlm rabe  yasasu kneeling, nan PC tabada umarnin ayi musu bulala talatin talatin Kuma ta koresu..

Nan mlm rabe yashi aikinsa wato jinbarsu.

Sir Aliyu kuwa gani yyi hukuncin bemasa yaso ayimusu Wanda yafi haka.

Amma yak'udurta aransa suka dawo zasu sha wuya gunsa har suyi candy.

Nan yajuya yashige pink house wato dakin su Hafsat.........😍😍


HmmπŸ€”πŸ€” bantaba tunanin haka  NIDA D'ALIBATA yake da masoyaba sai yanzun naga comments dinku da yawa musammun yan amintattun mata, insha Allah kullum zakusami page 2 arana ,safe da marece nagode sosaiπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

Share pls
[12/9, 2:59 PM] Aysha Galadima: NiDA D'ALIBATA

🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ13&14

Yana shiga yahango, Hafsat kwance tana rawar sanyi, Fatima nagefenta tana kukantausayinta.

Da sauri ya isa, yasa gunsu,kamshn turaren sa yasa Hafsat tagane yana gun.

Da sauri ta bud'e udanunta,hawaye na zarya afuskarta ta kallesa.

Shima k'uri yyi mata yana Kallo ,idanunsa sunji jajir ,jijiyoyin kansa duk sun tashi rad'o rad'o

Matsawa yyi yasa hannunsa yajanye gefen hijab dinta, yataba gefen wuyanta.

Aiko yaji da zafi, kallon Fatima yyi yace kamota muje hospital.

To Fatima ta ce, shikuma yafita,nan ta kamata suka biyosa.

Har get nan yabud'e  gidan baya ,yace Fatima ta sa Hafsat ciki ,nantasata itakuma tashige gaba.

Bayan sun iso hospital din ,sir Aliyu yafita , Jim kad'an yadawo ,da wata nurse da kujerar tura marar lfy.

Nan akasa Hafsat sai gun likita, nan sir Aliyu yyimasa bayanin dukane.

Bayan yyi bincike ,aka kaisu wani daki akasa mata drip ,akabashi paper yasiyo mgni da allura.

Nan yabar Fatima, yajuya XE tafi, muryar Hafsat tadaki dodon kunnansa tace Sirrrrrrrrrrr!

Juyowa yyi yaga tana kuka, cikin damuwa yakarasa gunta ,yace mene ne?

Ko jikin ne? ahankali yace ba tafiya zanyiba ,mgani zankarbo kinji, ga Fatima nan kusa dake ,bara naje.

Daga kanta tayi alamar to, nan yafita,sai sannu Fatima ke mata.

Bayan 20 minit suna nan ,hafast na kwance Fatima na zaune,sir Aliyu yashigo tare da doctor.

Da ledoji a hannunsa, nan doctor ya buda ledar yahada allurai

Hafsat naganin haka ,ido ya raina fata,dan tana tsoron allura.

Kallon Sir Aliyu tayi taga yakafeta da idanunsa, cikin muryar shagwaba , tabatason tana da itaba ,

Tace sir pls banason allura , kada kabari ayimun !

Tausayi tabasa amma sai yace hmm yanzun kuwa za,a miki  danki sami saukin jikinki.

Nan doctor yace ta gyara ayi mata,

Sir Aliyu tsintar kansa yyi da beson doctor din yyimata allurar a kugu.

Dan haka yace ayi mata ga hannu.

Nan ta runtse idanunta ,ta mik'a hannu tana hawaye.

Wata kara tasaki jin ansoka mata allurar.

Sir Aliyu har cikin kansa yaji karar.

Nan dai akagama ,sannan yace inta tashi dg bacci ,taci abinci tasha mgani ,doctor din yafita.

Sir Aliyu yakalli Fatima ,yace ,bara naje nayi sallah,inta tashi ga abinci nan kuci  kinji.

To tace sannan yafita, takalli Hafsat taga tayi bacci,nan tashige toilet din dake dakin tayi alwalla.

Bayan ta idar da sallah ta zauna,tanajin tausayin kawar tata.

Bayan2 hours  har Hafsat ta farka taci abinci da magani ,Kuma taji karfin jikinta sosai.

Suna nan zaune itada Fatima  sir Aliyu yashigo gab da magrib.

Yyi sallama ,yace yajikin ,kallon sa tyi tace da sauki sosai .

Ok bari nakira doctor ,aiko saiga shi ma yashigo, nan yaba sir Aliyu takardar sallama yace tarik'a shan mgani alokaci.

To sir Aliyu yace sannan yakallesu yace muje ko.

Nan suka bisa ,Fatima tayi saurin shiga baya Hafsat ta zauna agaba.

Bame mgana sai kirara ar. katun alk'ur ani ketashi .

Parking yyi gun wani guri inda akesaida nama gasasshe, yasiyomusu had'e da ice cream.

Yadawo ,suka cigaba da tafiya,bayan sun iso skul yyi parking Fatima tayi saurin fitowa.

Mik'amata ledar yyi yace rik'emuku wannan,godiya tayi tarufe k'ofar.

Hafsat ma ahankali ta bud'e kofar tace sir nagode sosai da taimakonka gareni.

Kataimaki rayuwata ,kabimun hakkina, kanuna cewa inada daraja Bacin  ni bakowa bace.

 Bason da bakin da zangode makaba,tana ida fada ta fito a motar.

Tabi Fatima  suka wuce hostel,

Shikuwa sir Aliyu ,shiru yyi yana. Mamakin mahanganun Hafsat ,jiki ba kwari yaje ya mayar da motar anakin get yyi       masaukinsa.

Washe gari ,alhmdllh Hafsat tasami sauki, bayan ta shirya ,tayi kalaci tasha magani.

Saita tsinci kanta da son xuwa office din sir Aliyu dan  ta sake yimasa godiya.

Nan ta tashi ta nufi area class , cikin sa,a tasami office in abude.

Nan ta shiga tayi sallama ,Turus tayi ,tare da jin gabanta yafadi batason daliliba.


Sakamakon  wata yarinya kyakkyawa ,zasuyi sa,o injuna da ita ,zaune kan cinyar sir Aliyu sai surutu take masa ,da yunifoam na yan day skul ajikinta.

Inbaccin da yarinyar tadago taganta databar office in .

Shima da kansa keduk'e yana latse latse a loptop yaji sallamar amma be dagoba.

,sa,ada ta kallesa tace yaya wacece wannan,tana nuna Hafsat?

D'agowa yyi, yaga Hafsat, saiyaji beji dadin dataga sa,ada acinyarsaba.

Amma sai bai nuna hakanba ,ahankali yace  sunanta Hafsat.

Sannan yakalleta yace yajikin da sauki tace ,sannan ta Duka tagaidashi.

Bayan ya amsa yakalli, saada yace ke autar Momy kidagani haka  nan,

Kije driver yakaiki skul kada kiyt latti.

Turo baki tyi tamike tace ai mommy ta matsa nakawo maka break.

Nan ta tafi,itama Hafsat ta yi  hanyar waye ,ahankali yace ke zonan!!!!!

A next page zakuji  shin wacece Hafsat?
Kuma wanene sir Aliyu?

share pls
[12/9, 6:33 PM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ15&16

Wannan page nakine  my bestie nah ameera marubuciyar ramin mugunta, kiyi yadda kkso dashi,ina mugun yinki irin sosai din nan🌹


Ahankali ta tsaya, cikin husky voice insa metada hankalin yan mata yace bazakizoba?

Saurin juyowa tayi tace ah ah sir ,yi hakuri , nan taxo ta duk'a gabansa.

Kallon ta Yy yace  yanuna basket din dake gefensa ,yace yi serving d'in kanki.

Da sauri ta d'ago kanta ,yakafeta da mayun idanunsa ,saita sunkuyadda kanta.

Ahankali tace sir nakoshi saida na yi  break a hostel.

Batare da yakalletaba ,Yace miyasa kikeson yimun musu ko gaddama,

Natsani ayimun musu ko gaddama ,dama jiya kinbatamun raiko shine zaki sake batan ko?

Da sauri ,tace  sir bahaka bane, nasaba bana iya cin abincin ni daya sai cikin jama ,a muci atare.

Inni dayace bazan iyaciba,

Kallonta yyi Yace  bari nayi serving dinmu muci atare ko?

Da har zatace ah ah ,ta tuna bayason musu ,sai tafasa.

Plate yadauka da kula yyi serving dinsu Chip's ne  sa kaji soyayyu ,

Kafeta yyi da ido Yace taso muci nibantaba break a 7:30 ba sai yau.

Kan duguwar kujerar dke office in ,ya zauna yasa plate in agabansa da cokali me yatsu.

Ahankali tazo ta zauna ,duk da abincin yaburgeta Kuma bata saba cin irinsaba.

Amma badantaso suci tareba ,saidan kada tabata masa rai,gashi shikuma yana kyautata mata.

Ahankali tyi bissimilla tafaraci saidai taki yarda su had'a ido dashi.

Shikuwa cin abincin sa yake tsakani da allah yana latsa wayarsa.

Can yadago yasaci kallonta yaga bata kallosa ,aiko yyi mata k'uri da ido.

d'an karamin bakinta yake Kallo datake tauna abincin kamar bata son ci.

Azuciyarsa ca yake nifa ban taba ganin yarinyar nan tayi make up ,ko kwallima bata ahafawa, datana kwalliya aisaitafi haka kyau.

Lallai maza ba sa gabanta ,karatune agabanta, tsaki yyi Yace to ni meruwana da hakan.

Aje spoon d'in tayi ,da sauri yadago Yace banganeba .

Cikin shagwaba ta ce yaya na k'oshi  cikina kamar zai fashe,tafad'a tare da mik'ewa tsaye jin anyi ringing shiga class dn yau bbu assembly.

Har ,aransa yaji d'adin yayan datakirashi dashi,amma azahiri sai ya yatsina fuska.

Yace waye yayan ,lallai kinzama yar kalan dangi.

Turo baki tayi tace ah ah, niba kalar dangi nayiba ,nasandai ka girmeni nesa ba kusaba ,shiyasa nacema ka hakan .

Kuma wadda ta fita yanzun itama haka aitacemaka , tafakaici idonsa ta gallamai harara.

Sarai yaganta ,cewa yyi nikeke hara ko? Ya matso gab da ita har sunajin numfashin juna.

Matsawa tyi  bakin kofa tajuyo tayimasa gwalo  ta ruga aguje tna dariya.

Shima dariyar mugunta yyi Yace haba yarinya zankamaki ,zakisan Wanda kka ma gwalo.

Zaunawa  yyi ,yafara tunani ,shinmeyasa yake kulada da duk wani al,amari na Hafsat?

Miyasa bayason ganinta cikin damuwa, Kuma bayason yaga ana cutar da ita??

Duk yadda yaso yadena kulata ,da yaganta saiyaji kosan su rabu bayaso.

Wata zuciyar tace masa, shakuwace kawai,  da haka ,yadauki taxt book ya tafi ss2A.

***********

WANENE SIR Aliyu

Aliyu Suleiman  rabo ,shine cikakken sunansa,

d'ane ga alh Suleiman rabo senator na Kaduna, su 4 agun iyayansu.

Shine babba sai k'annansa ,kabir da sadik ,sai autarsu sa,ada.

Yayi digree  dinsa na1 dana2 A ingila ,yakaranci fannin capinter ,yanada company dasuke kera furniture na gida DNA waje.

Dakuma abinda yashafi parlour, da kayan decoration na gida.

Suna zaune a unguwar gwamnati  dake Kaduna,

Hjy Aisha itace mahaifiyarsu mace ce mai son jama,a bbu ruwanta da cewa sai mai wadata  zatayi hudda dashi.

Akwaita dason taimakon talakawa,hakama  mijinta asalinsu yan yolane ,aiki yamaido su Kaduna ,har sukadad'e alh Suleiman yazama senator.

Dalilin dayasa  sir Aliyu yazo makarantar su Hafsat koyarwa ,shine governor yanasamun korafe k'orafe akan yan  boarding skul  ana xalintarsu.

Akan abubuwan da gwabnati kebasu ,ba a basu  ,Kuma babu tsaro skul din da malaimai da suke koyarwa.

Kuma ba abincin kirki,hakan yasa governor, yatura amintattun yaransa amatsayin teachers dan su  dauko masa da ruhoto.

Abinda yadace  agyara agyarashi.

Kowace  skul boarding dke Kaduna antura malami2 Kuma ba Wanda yasan wani amalaman.

To shine ,senator yaxo da maganar cikin familynsa nan sir Aliyu Yace zai iya.

Ba6ata lokaci, senator yagabatardashi gun governor,

Kuma governor yyi murna ,da akasamu nagida ,nan Sir Aliyu yasa hannu a skul dinda zaiyi teaching.

Dama shekara  2 akabasa, nan akakaisa skul din dake cikin k'auyen Kaduna, akabashi gd a step quarters

Dakuma hadadden office, din da zai zauna ,sannan ,yazabi subject din dazai rik'a koyawa.

Lokacin daya shiga skul din yalura da ss3 basuda kunya da tarbiya sai wani kallon sa suke ,atake yaji yatsanesu.

Dasu zai dunga koyamawa ,sai ,ya yafasa yacigaba da koyarda ss2 dukda suma saida yyi musu Jan ido.

Duk week end yake xuwa gd  yadawo ranar Monday.

Hjy Aisha wato mahaifiyarsa da bataso yyi nisa  da asu taso hana teaching din amma  daddynsa Yace ah ah said yyi.

Sir Aliyu mutumin kirkine  sosai cikinsa da wajansa Kuma  miskiline na k' arshe  .

Bayason shishshigi bayashiga abinda beshafesaba.

Sannan kwata kawata  mata basa gabonsa dan har yanzun babu macen daya taba cewa yanaso.

Iyayensa sun so yyi aure amma yak'iyi da ammasa mgna sai Yace besamu wadda tayi masaba.

Har akafara tunanin ko beda lpia harde akagane qalau yake.

Dadinsa kuwa so yake duk wadda yasamu me tarbiya kawai yahadasu aure  tunda yakiyi,

Kafin yazama tuzuru.

Sir Aliyu yanason familynsa sosai yashak'u da iyayensa musammun mahaifiyarsa  tana k'aunarsa.

Kuma tanaji dashi, acikin k'annansa yafi shak'uwa da sa,ada.

Bata jin kunya ta hau cinyarsa tana masa shagwaba yana biyema  ta,yasiyo mata Wannan yasiyo mata wannan

Dukda shekarunta basufi 15years  ba sunshaku sosai,amma duk da haka tana mugun tsoransa,

Dan sir Aliyu ba wasa,inna yan miskilanci suka motsa ko sa,adar baya kulawa, Wannan shine labarin sir Aliyu.

WACECE HAFSAT.....

share pls
[12/10, 4:38 PM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ17 &18

Wacece Hafsat?

Hafsat yarinyace yar kimanin15 year, farace ita kyakkyawa ajin farko,

Itaba gajeraba,bakuma doguwaba,tana da hanci da d'an karamin baki,sai girarta me gashi sosai harta kusa had'e wa.

Tana da dara daran idanu inta lumshesu tana kara kyau ,akwaita da sanyi Hali ga kirki.

Mlm Aminu shine mahaifinta ,suna zaune a unguwar kawo dke Kaduna

Mlm aminu talarkane lik'is ,yanzun matarsa 1  tana da yara2 . wato  inna Laure.

Mlm aminu sun hadu da mahaifiyar ,Hafsat agarin gombe, suka fara soyayya, inda kawunanta suka bayar da,ita ga mlm aminu.

Kasancewarta marainiya ba uwa ba uba.

Bayan andaura auren mlm aminu da Maryam wadda akafi sani da mairo.

Yatafo da ita Kaduna, suka cigaba da zama cikin so da kauna.

Bayan shekara 2 mairo ta haifi yarta wato Hafsat,

Bayan Hafsat batasake haihuwa ba, hartayi shekara6 .

Nan fa mlm aminu yanuna yanason haihuwa.

Ba bata lokaci yace aure zaiyi, mairo batayi masa gaddamaba.

Nan yanemi inna Laure dake zawarci Kuma ,yar uwarsace ya aureta.

Bayan auren ,inna Laure ta lura da  Mlm aminu yanason matarsa da yarsa sosai baya wulakantasu.

Dama ita tazo gidan da niyar fitar da mero,kota halin kaka.

Dan haka tayi makirci amma abun ba armashi , dan haka saita canja shawara, ganin tanada juna biyu.

Akwana atashi bbu wuya awurin uban giji,yau inna Laure ta tashi da nakuda.

Dan haka kafin takira mairo ta zo ta taimata mata ta tanaji wuk'a ta boye.

Bayan ta kira mairo,cikin ikon Allah ta haifi d'a nmj Kuma mlm aminu bayanan.

Nan aka aiki Hafsat takirasa ,Aiko suka taho tare ,Laure najin sallamarsu.

Tayi ihu da kara tafiddo wukar nan tayanki gefen hannunta.

Lokacin mero tagama shirya yaron yana hannunta.

Tayi saurin rike Laure  ,Dede nan mlm aminu yashigo .

Nan Laure ta ture mairo tana kuka tace gara da Allah yakawoka sotake takashemu nida yaronka.

Gashi harta fara yankana,salati yy ,itakuwa mairo mamaki yahanata mgna.

Atake yyima mairo saki2  yakoreta yace tabar masa gidansa da yarsa.

Hafsat naji nagani akarabata da uwarta, alakacin tana yar8 years.

Nan rikonta yadawo gun Laure,inda duk aikin gdn yadawo kanta.

Ga tanasa mata talla,da farko mlm yahana ,dg baya data hadasa da boka yabari hardashima ake  hantararta.

Akwai makwabcinsu alh Nasir me haline sosai yanada ya' Fatima, tare suka tashi da Hafsat sun shak'u da juna.

Duk yan gidansu Fatima suna tausayin halin da Hafsat take ciki .

Haka tacigaba da azabtuwa da shan wahala gun Laure sannan intake  rainon danda Laure ta Haifa.

Ana haka tagama primary skul, alokacin Kuma Fatima ta gama itama amma boarding zata.

Tasoma Hafsat itama taje amma inna Laure ta hana.

Mahaifin Fatima shiyasama  mata day skul tacigaba da zuwa intaje yau gobe bata xuwa sbd ukubar inna Laure.

Shikuwa mlm aminu yazama mjin tace.

Ana haka ,inna Laure ta sake haihuwa tasami mace ,hanifa ,

 Akuma lokacin Hafsat tayi JSCE  itada Fatima.

Nan Fatima taita had'a  abbanta da Allah akan yaje yasami mlm aminu akan yanason yakai Hafsat boarding.

Nan abbanta ya yarda kasancewar anaji da Fatima,itada yayanta ,Ahmed  sukadaine agun iyayansu.

Bayan abban Fatima yyi ma mlm aminu bayani haryaki yarda dan yason Laure bazata yardaba.

Se abban Fatima yyi masa dubara yace dg skul dinsu hafsat   gwabnati tazabeta ,inkuma zaiyi musu adaureshi bbu ruwansa.

Atake ya  yarda, nan yaje yyima Laure bayani da harta fara  bala ,I  taji ance gwabnati aisaitayi tsit.

Nan abban Fatima yyimusu komai tare da Hafsat aka kaisu  ss1 ,class daya ,house daya.

Ko tsinke mlm aminu betaba siyama hafsatba .

Abban Fatima tunda yyi mata siyayyar farko besake mataba dan yadauka mlm aminu yana mata.

Itakuma Hafsat ta hana Fatima ta fad'i   dan haka ,duk abinda aka kawoma Fatima dashi suke amfani.

Suna haka  harsuka shiga ss2  sannan sir Aliyu yazo skul din.

Duk sadda sukazo Hutu  sai Hafsat taci ukuba kafin takoma.

Sannan  akwai wani tantirin dan iska waishi deeni gidoga.

Dan yayar inna Laure ne tunda yaga Hafsat ta girma yanuna yanasonta.

Itakuma batasonsa sbd ba mutumin kirkibane.

Itakuwa inna Laure catake ta bashi ,dan dama burinta Hafsat tasha wahala ta tozarta arayuwa.

Wannan ne labarin Hafsat.
_______________

Cigaban labarin "

Bayan kwana2, Hafsat ce zaune akwanarsu tanata tunani,

Yau kwana2 kenan rabonta da sir Aliyu , anya yana lfy, gaba daya saitaji skul in duk bbu Dadi

 Dan tun ranar da tabar office insa da gudu tayimasa gwalo rabanta dashi kenan.

Dama ranar basudashi a class dinsu,jiya da yau Kuma sunadashi amma be zoba.

Tashi tayi tasa ka hijab dinta ,ta fito ta nufi  area class.

Alokacin karfe2:30 pm.

Dede staff room ta tsaya ganin mlm rabe zai rufe, nan ta je ta gaidashi.

Amsawa yyi ,zai juya yatafi,da sauri tace mlm  wai ina sir  banganshiba kwana2.

Dukda tana tsoron kada yyi mata wata fahimta.

Kallon ta Yy yace wai baki saniba ,aibashi da lfy ,yana gidansa dake step quarters.

Yanzun haka ,kinga ga doctor can zan kai yadubasa.

Muje ma ,kin kuladashi matsayinki na yar uwarsa.

Dan shi mlm rave atunaninsa ,Hafsat kanwar sir Aliyu ce.

Kallon sa tayi tace mlm ai anhana zuwa step
[12/10, 9:00 PM] Aysha Galadima: NiDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ19&20

Wannan page nakune yan NIDA D'ALIBATA fan's kuyi yadda kukeso dashi,inamugun yinku irin sosai din nan😍😍

Kallon sa tayi tace mlm ai an hana zuwa step quarters.

Girgiza kansa yyi yace ,aini ke dukan dukan duk Wanda yaje ,

Nabaki izni kije ki kula da yayanki,aike yakamata kije matsayinki na muharra marsa.

Itadai Hafsat shiru tayi tana,tunani wai itace muharramarsa.

Amma ta k' agara taje taga yajikin nasa yake.

Mlm rabene yace muje ko,da sauri tadawo tunaninta tabi bynsa.

Nan doctor din yabisu,  suka dauhanyar step quarters.

Tun daga k'ofar shigowa sukejin kakarin amai,Aida sauri suka shige.

Duke' gaban tape din gidan suka samesa yana amai kamar ze amaye yan cikinsa.

Kuma aman yellow ne,da sauri Hafsat ta isa gunsa.

Cikin tausayawa tace sir sannu,d'agowa yyi yakalleta yamayar da kansa.

Buta ta dauka ta Tara jikin tape din tacika,ahankali ta tsugunna kusa dashi,

Tana xubamishi ruwan yana wanke fuskarsa da bakinsa.

Mlm rabe da doctor suka shiga parlour sunajiransa.

Kallon sa tayi taga ya dan rame fuskarnan tayi fiyau har dan yellow take.

Ahankali yace hafsattttttttt!!

Har cikin kanta taji sunan ,ahankali tace sir sannu!

Kallon ta Yy yaga tana hawaye, murya asark'e yace ,meyene nakuka ai nasami sauki ko.

Waye yasanar dke ne? share hawayenta tayi tace mlm rabe ne.

Kallon ta yyi yace to muje ,amma banaso kisake kuka nafa sami sauk'i kinji.

To tace tabi bayansa dan shiga parlour, kallon sa tayi taga  shirt ce da 3quarter ajikinsa.

Jikinnan nasa amurde yake ga gashi kwance baki k'irin ajikinsa.

Bayan sun zauna doctor ,yazo yafara treating d'insa.

Yarubuta masa mgni ,sannan yyi masa allura ga hannu,dg karshe yace yarage tunani.

Nan sir Aliyu yaba mlm rabe takardar magani dan yasiyo, sukayi sallama da doctor.

Dazasu fita mlm rabe yace ke Hafsat ki zauna kkula dashi , yakalli sir Aliyu yace ashe batason baka lpia ba,

Saida ta  tambayeni kana ina nafada mata.

Murmushi sir Aliyu yyi yace ainasami sauki mlm, nan suka fita.

Hafsat bataso mlm rabe yace wai taje nemansa,tasan sir da disgi kadama yyi mata wata fahimta.

Shikuma Sir Aliyu ,samun kansa yyi da jin dad'in yadda Hafsat tadamu dashi ,gashi har kuka tayi masa na tausayinsa.

Hafsat tashi tayi , sir Aliyu yakalleta yace ina zaki, azuciyarsa ca yake Allah yasa kada ta  tafi.

Tsintar  muryarta yyi tana cewa, zan dan shiga kitchen ne sai in gyara gidan.


Yaji dad'in hakan har cikin ransa amma afili sai yace .

Nifa bana cin jagwalgwalenki, kinma iya girkine?

Bata ce komaiba tafita,azuciyarta tace oh mutumin nan ba,a iya masa, beda lafiyar amma jin kansa na nan.


Tsakar gidan ta share ta goge, tana bakin tape zata d'ibi ruwa, mlm rabe yashigo ,ledar magani yabata yace kibasa kice sai yaci abinci ,yasha.


To tace ta kar6a , shikuma yafita, parlour takai maganin tasami sir Aliyu baya parlour n.

Ajewa tayi ta fita tashiga kitchen, taga akwai komai na bukata.

Dubawa tayi taga electric da risho, nan ta kunna risho ,ta  aza tukunya kafin ta tafasa tagyara wake.

Nan taxuba waken tayi dan jajjage a greater, tatsane waken bayan yazabku

Tasoya kayan miyan  ta zuba  kayan k'amshi da maggi.

Nan dai cikin 1 hour ta yi masa faten wake da dankalin turawa ,yaji kifi da alaiyahu.

Tuni gidan yadau kamshi,nan ta wanke kayan data bata.

Tun cikin bed room  sir Aliyu kejin kamshin girkin  nan,

Har parlour yafito amma kamshin karuwa ,yake .

Atake tsohuwar yunwarsa ta taso yaji yakagara yaci abincin ko zazzabi nsa yasauka.


Befi minti gomaba da zamaba, ,tashigo da kula da plate da serving spoon.

Zaunawa tayi gabansa tace sir mlm yakawo magungunan ,amma yace saikaci abinci.

Sannan kashasu, yatsina fuska yyi yace ok sai anjima innaje restaurant naci.


Turo baki tyi tace gara abinci na mararsa lfy kaci pls nyi serving dinka?

Ah ah,Yace  ahankali tace meyasa sir,

Kallon ta Yy yawani langabe kai kamar wani yaro,yanunata.

Yace bakece kika dena cemun yayaba, aikinga bazanci abincin wadda bata daukeni yayantaba.

Dariya yabata sosai  amma sai tadaure tace, bakaine kacemun yar kalan dangiba.

Murmushi yyi Yace tskanarki fa nake,
Kallon sa tayi tace to yaya zakaci abincin ko?

Kaga saikasha magani, haka doctor Yace,kafeta yyi da firgitattun idanunsa yana Kallo, yajin dadin yadda take lallabasa.

Kallon ta yasakeyi Yace,akwai sharad'i ,inkinyarda to zanci.

Azuciyarta tace ,towai dole saikaci abincin ne xakace saida sharad'i.

Amma a fili saitace meye sharadin Yace kinyarda muci atare.

Da Sauri tace ah ah banajin yunwa ai.

Had'e rai yyi Yace ok zaki iya tafiya,  tunda bazakbi umarnina.

Murmushi tayi tace ,tsokanarka nake,fa nan tabude kular.

Tsaki yyi Yace tunda ga abokin wasanki ko,aidama ina hagwanki,amma zankamaki,zakison Wanda kikayima gwalo rannan.

Kamshin girkinne yadaki hancinsa yalumshe ido.

Bayan ta xuba musu a plate daya, tasa 2 spoon,  tace bisimilla yaya.

Nan suka zauna kan carpet, suna kwasar girki.

Sir Aliyu har wani lumshe ido yake dan girkin very nice.

Can yasaci kallon ta yaga itama ba laifi cin abincin ta take.

Kuri yyi mata ,ganin ba hijab ajikinta da dankwali.

Gashin gaban goshinta yatashi iskar fanka na kad'asa gwanin sha,awa.

Ga doguwar rigar check pink dinta tabi jikinta,

Ganin zata kallesa yasa yadena kallonta.

Nan suka cigaba da cin abincin su har suka gama,nan takwashe kayan,

Ta fito  ta kai kitchen, a window din kitchen din taga inwarta ta glass ba hijab da dankwali akanta.

Aratsane tayi sallati ,ta duba gefen datake tsaye taga dan kwalinta da hijab dinta.

Tunawa tayi d'azu tacire dazata aza girki da sauri tasaka, ta dauki swan water roba1

Dan kai masa yasha mgani, tana xuwa yaganta da hijab,aransa yace, k'ila dazata  aza girki tacire.

Nan ta basa magani yasha ,bata kallesaba dan ta ji kunya daya ganta ba hijab da Dan kwali.


Tace yaya kaje ka kwanta kayi bacci.

Kallon ta Yy yace ni Kallo ma zanyi, sannan kina kallon wani gu kinamun magana.

Bazaki kalleniba , cikin shagwabar da batason tayiba ta mik'e tsaye tace,

Pls nidai kaje kayi bacci, zakafi samun saukin jikinka.

Juyawa yyi yanufi hanyar bed room ,sakamakon wani yanayi da yatsintsi kansa jin yadda take shagwaba.

Gab da zai shiga yace ,innayi baccin ina zakije?

Tace yaya zan koma hostel ,har hudu fa tayi.

Kallon ta Yy yace dama ba jinyata kikazoyiba  ko,

Saiki tafi kawai hakan yyi kyau.

Bejira amsartaba yashige bed room.....

Share pls

[12/11, 9:16 PM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ21&22

Tsaye Hafsat tayi ,tayi shiru ,axuciyarta tace oh yaya fushi yyi kenan, Toni  nafasa tafiyar.

Dan haka toilet na tsakar gd ta shiga tayi alwalla tazo, parlour tayi sallar la,asar.

Bayan ta idar, ta fito ta nufi kitchen danyima Sir Aliyu girkin dazaici da dare.

6angaran sir Aliyu kuwa ,yanashiga bed room toilet yashige yyi wanka da alwarla.

Bayan yyi sallah yacire jallabiya dg shi sai 3 quarter yakwanta.

Tunani yake meyasa yadamu dan Hafsat ta tafi?

Wani 6angaren na zuciyarsa haushin kansa yakeji ,akan
Yadda yadamu da ita, 

Tsaki yaja,danshi atunanunsa ,ta tafi hostel , yana nan kwance har bacci yyi gaba dashi.

Hafsat bewar allah tanacan kitchen tana hak'ilon girka masa sakwara da miyar agushi.

Sai sauri take batason magrib tayi mata agidan sir Aliyu.

Ba,ita ta idarba sai 6  saura, tasaka komai ature takai parlour.

Sannan tashiga bed room din,kwance tasamesa ba Riga, ga uban gashi kwance a faffad'an kirjinsa.

Ta d'an tsorata  dan bata saba ganin babba ahakaba, amma arantace oh ji mutum ko ina jikinsa gashi.

Da sauri tadawo bakin k'ofar shiga dakin ,ta bada baya ta shiga knocking ahankali.

Da addu ar tashi da ga bacci ,yafarka abakinsa, jin knock yasa yakalli k'ofa.

Amamakin sa yaganta tsaye ta bada baya.

Tsaki yaja yace ke lfy ,zakiyimun wani tsaye, meyasa kika dawo dakka tafi?

Batare da ta juyoba tace katashi magrib takusa, ga abincin da zakaci nan da dare ni xan tafi.

Haushin kansa yaji, da ya6a mata magnar da yayi,ashe da bata tafiba.

Ahankali yace muje na rakaki sarkin jin tsoro, kamar yason abinda ke ranta.

Dama sotake tace yarakata sbd tanajin tsoro,amma tanagudun fad'a masa ya disgata.

Jallabiyarsa yasaka ,yasameta a parlour ,nan yafito tabi bayansa ,

Wani gun amfara, kiran magrib,ahanya yace ke bakauya kincika tsoro wlh.

Sarai tasan Jan maganane sai ta sharesa, har gab da hostel yarakota, anan sukaga Pripet din da aka kora nashigowa da kyansu.


Kallon ta Yy yace ke ni nakoma, ahankali tace, Allah yak'ara sauk'i,saida safe.

Kallon ta Yy yace ameen ngd kinji, bejira amsartaba yyi gaba.

 Ita kuwa daki ta wuce, tasami Fatima zata yi sallah Fatima, tace sis ina kkje tun dazu naketa nemanki.

Zama tayi tasanar da ita,ai sir Aliyu ba lfy, nan ta jajanta mata, Hafsat taje tyi alwalla tazo tayi sallah.

Washe gari byn sun gama shiryawa ,suka nufo area class, Aiko hadu da sir Aliyu xe bud'e office insa.

Nan Fatima ta ce lah sis ga sir can ze bud'e office yamaji sauki ,muje mu gaidasa da jiki.

Nan suka nufi office ,nasa bayan sun gaidashi sukamasa yajiki,suka fito,yaso yatsayadda Hafsat ,

Amma ganin ba ita1 bace yakyaleta.

********** bayan kwana2 sir Aliyu yawarware yasami sauki sosai, 
Ya Tara Pripet, yasanar dasu kullum,sai sun share staffroom

Sun wanke toilet na malamai, sun share bakin get,

Kamar su mutu dan bakin ciki, bbu damar su Musa masa dole suyi,wani sabon tsanar Hafsat suka sake ji.

Yau Yakama  talata, kullum sir Aliyu ,a step quarters yaje kwana ,amma yau saiyaji yanason kwana,

A office nasa sbd akwai bed room, aciki ,dan haka bayan isha,I yaje yakwanta can..

Da misalin karfe1:30 am,katti3 suka shigo skul din, kasancewar ba wadatattun masu gadi.

Gaba daya sun hargitsa skul in, sai ihu kato ake, ,students sun hade gu 1  bbu zancen wni Senior retie.

Atsakiyar makarantar inda suke ihun nan kattin suka zagaye su suka nuna masu wuk'ak'e, da sanduna akan sun atsu.

Dayan cikinsu ya kunna touch light, yana haska students koxaiga wadda ta yi masa,yabiya bukatarsa da ita.

 Nan yafito da wata ss1 da ss 3  yasake haskawa cikin rashin sa,a yahasko Hafsat, atake yakwadaita da ita  dan tanada kira me daukar hankali.


Fisgota yyi yanuna mata wuka, yafito da ita,tsabar kad'uwa saida Hafsat tasaki fitsari.

 Atake students duka suka saki uban ihu ,kasancewar dare ko ina saida ya amsa.

Sir Aliyu kuwa cikin baccinsa ,yaga Hafsat tana kuka tana kiran sunansa yazo yatai maketa.

Atake yafarka ,yyi sharkaf da zufa ,dedenan Kuma yaji ihun students.

Da sauri. Yasaka jallabiyarsa ,afili yace skul din nan ba lfy wannan ihu haka, mlm rabe yakira, yasanar dashi su hadu a hostel dan bbu lfy.

Nan yace gashinan ,shima yaji kamar ihun students, kasancewar shima mlm rabe yana cikin step quarters na makarantar.

Da sauri. Sir Aliyu yafito yana haska wayarsa, jin ihun yyi yawa yasa yahada da gudu,

Yana shiga hostel  din yabi inda yakejin ihun students, yana shan kwana, yahangosu sun cure gu1

Sannan ga wasu maza biyu da wukake ahannusu suna nuna masu.

Agefe Kuma ga wani yana cire kaya ga yaro 3  gefensa.

Innalillahi wa inna ilaihir raju, kawai yake maimaitawa atake yagane meke shirin faruwa.

Ai da sauri , yaciri wani rashe na bishiya dake bayansa batare da yaji tsoroba ,yasa wayarsa a aljihun wandonsa.

Da sauri yayi gunsu ,Dede nan dayan katon yyi gun daya daga cikin 3 dke gefensa.

Amamakin sir Aliyu ,sai yaji muryar Hafsat tana cewa wayyo Allah na yaya aliyu  kazo katai makeni.

Kada suketamun haddi, yaya Aliyuuuuuuuuuuu!!!

Ai azabure had'e da fad'uwar gaba  sir Aliyu ya ida isa kamar wani mayunwacin zaki,abunka da karfeffen mutum.

Hannu 1 yasa yadamk'osa ,sannan yasa ,reshen dayaciro yabugo sauran kattin dasuka nufosa .

Dan ceton dan uwansu,atake suka fadi kasa ,

Wani wawan punch yakaima na hannunsa a fuska ,yasake masa,

Atake bakinsa yafashe da hancinsa yafadi awahalce,

Sannan sir Aliyu yacigaba da suburbud'ar biyun dake  kwance,

Akuma lokacin Hafsat ta fahimci sir Aliyu ne ,yakawo masu wannan agajin.

Da sauri ta buya abayansa tasa  hannuwanta ta xagaye cikinsa,

Tana abayansa ,yacigaba da suburbudarsu, kamar actor nadukan yan gidan both lolx....

Duk students sunyi mmkin jarumtar si aliyu, shikuwa mlm rabe tsaye yyi yana ganin ikon Allah.

Dan bayan yafara dukansu yazo

Cikin 15 minit Sir Aliyu yabazar da kattinnan 3  nan mlm rabe yazo da igya ya dauresu.

Gaba daya Hafsat ta rud'e kuka kawai take, ta lik' e jikin sir Aliyu. Wai sai ya kaita gidansu ,kamarma bata hayyacinta.

Sai dukansa take akirji akan yakaita ita de gidansu.

Kok'arin rabata yake da jikinsa , amma sake manne mai take.

Mlm rabe ne yace  mlm gsky bata hayyacinta ,tunda taki sakeka ,kaje da ita gdanka ta kwana ,

May bee ansan yadda za,ayi dasafe ,amma  ko ka barta hankalinta bazai kwantaba,

Tunda dai k'anwarkace inaganin ba matsala.

Nan mlm rabe yacema students ko wacce ,ta tafi d'akinsu.

Fatima kukan tausayin.kawarta kawai take, haka ta tafi daki jiki ba k'wari.

Akan dole sir Aliyu ,yaja Hafsat ,kamar cingam suka tafi a step quarters.

Ko acanma  babu  yadda beyiba da ita akan ta kwana bed room, shi yatafi parlour.

Amma Hafsat tasa rigima ,ita gunsa zata kwanta,lura yyi da kamar bata hayyacinta yasa  yakyaleta.

Ken bed din yakwanta tare da janyota Jikinsa ,

Yajamusu bargo,tareda shafar kanta ,itakuwa sai ajiyar zuciya take.

Wani kwance akan faffad'an kirjinsa,tasa hannunta daya ta zagaye cikinsa dashi.

Batafi minti 10 ba yaji tayi bacci, ahankali yazo kwantar da,ita gefensa, da nufin Yakima parlour.

Ai sai ta sake mannemai,aiba yadda ya iya haka suka kwanta.

Yanajinsa atakure dan betaba kwanciya da maceba a haka aayuwarsa sai yau.

Gaba daya tudin nashanunta sun tokaremasa kirji ga wani bak'on yanayi dayakeji atare dashi.

Addua kawai yake gari yawaye, lfy ko Hafsat tadawo tunanin ta,

Akan dole ya yard a su kwana gu daya dukda ya yarda da kansa, amma yasan shaid'an  ze iya  rays maka abu marar kyau.

Da wannan tunane tunanen bacci Yy gaba da shi,

Da misalin karfe5:30 am Hafsat ta farka da adduar tashi dg bacci.

Atake abinda yafaru yadawo mata, amma tyi zaton mafarki take.

Maido nefa akayi dakin yadauki haske ,kallon dakin tayi da sauri tajuya  junta jikin mutum.

Kawai taga sir Aliyu kwance yana bacci, abinda yafaru  jiya ta tuna.

Da sauri tabar jikinsa cikin jin kunya da ganin rashin dacewar hakan.

Ahankali yabude idonsa ,yaga Hafsat bata ,d'akin .

Da sauri yafito parlour, azaune yaganta tayi tagumi, ahankali,

Yace kintashi bata kallesaba tace eh ,yace jekiyi sallah lokaci yyi.


Tsakar gd  ta fito ta yi alwalla a toilet, tazo parlour tayi sallah.

Bayan ta idar ,sir Aliyu yafito dg bedroom.

Yaxauna kan kujra , yakalleta, da sauri tace yaya ina kwana?

Lpiaqlau  matsoraciya,turo baki tayi tace aide tsoro halak ne .

Tsaye ya mike yanufeta yana cewa  kin rainani ko,

Da sauri ta zura aguje atsakar gd yarufa mata baya,su ka hau zagaye gdan.

Har hatsat tagaji da gudu ta koma parlour ta fada kan kujera tana maida numfashi.

Biyota yyi ,said hakuri take basa,yak'i sauraranta.

Zama yyi yajanyota kan cinyarsa ,ya matse mata hanci da baki.

Sai mutsu mutsu take yak'i saketa.

Can tasa hannunta a hamurtarsa tafaramai  chakul kuli.

Da sauri yacikata yana dariya,had'e da aza kansa gefen wuyanta.

Har sajen fuskarsa na gugar gefen wuyanta, wani yanayi hafsat ,taji,

Da sauri ta kalli agogon bango tace yaya bara naje na shirya  har 7  tayi kada na makara.

Nan ta tashi dg jikinsa ,tasaka hijab ta fito, bata kallesaba ,tayi ficewarta xuwa hostel....


Ina godiya ga masoya  nida D'ALIBATAπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

Dan  Allah masu bina ta PC akan natura masu dg farko pls kutambaya agrps dina zaku samu.

Share pls
[12/11, 10:07 PM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ23&24

Tana isa hostel tasami ,Duka malamai da dalibai, da police, antaru ga kattin nan zahiri  suna a daure.

Nan principal tasa mlm rabe yakira  mata sir Aliyu, ba bata lokaci yyi masa waya.

Ba,afi minti10 ba yazo, yasha  kananun kaya sai zabga kamshi yake.

Gaba daya Kallo yakoma kansa , musammun ss3  kowace ji take inama yace ya k'yasa.

Nan malamai da principal suka jinjinamasa akan namijin k'okarin da yyi.

Sannan akatasa kattin gaba zuwa police station, dan ayi musu hukunci.

Sannan kowa ya watse ,Hafsat taje ta shirya suka nufo  class itada Fatima.

*******
Yau Yakama  Saturday, aranar Kuma ake visiting, kowa murna  yake  amma banda Hafsat dan tasan bazata ga  yan gidansuba.

Sir Aliyu kuwa yana gidansu week end, zaune yake kan dinning area ga Kula's agabansa na abinci.

Yyi shiru yana ta tunani,mommynsa ce wato hjy Aisha ta fito ta na masa magna amma bejiba yana tunani.

Bubbuga table din tayi  ,da sauri yakalleta yace my mommy.

Kallon sa tayi tace   babana lfy me damunka kwana2 naganka kana yawan tunani?

Murmushi yyi yace no mommy ba komai, yanxunma zan wuce a skul nayi mantuwa,

Da sai dare zantafi, amma  bari naje asamun abincin a basket.

Kallon sa tayi tace to, amma badan ta yarda bashida damuwaba.

Nan akasaka masa abincin a basket, yadauka, yasa agidan baya, yashige gaba yaja mota sai skul.

Hafsat na zaune a block din admin block,  tana kuka harda hawaye.

Tunani take azuciyarta,  tunda ta zo skul din bbu wani nata da yataba zuwa,wasu k'ayensu har ca suke basu taba ganin yan gidansu ba.

Saidai Fatima ,tace musu da safe ake xomata shiyasa.

Komai da ba Fatima suke amfani,ita tsoronta daya kada Fatima yau da gobe tagaza da ita.

Dukda bata tunanin Fatima zatayi mata hakan.

Amma tason dan Adam ,ze iya canjawa.

Sir Aliyu yyi horn aka bud'e  masa get , yashigo yyi parking,  yafito ra basket a hannunsa 

Yanufi office dinsa ,ya bud'e ,yashi ga, ya zauna, tsintar kansa yyi da son yaga Hafsat.

Tashi yy dan yasan yau ake visiting, yanufi gundake da students ko xai ganta acikinsu.

Kamar ance yakalli gefensa, yahango  Hafsat zaune tayi tagumi,tana kuka.

Yah salam! Yace afili da sauri yanufi gunta, ganin bata gansaba.

Yasa yarungume hannuwansa akirji yana Kallonta, k'amshin turaren sa taji da sauri ta d'ago kanta.

Idanunta tsab cikin na sir Aliyu, murya a sarke yace,hafsat ttttt!

Meke faruwa ,me Akamiki kike kuka haka??  Shiru tayi ,can Kuma tace ba komai.

Kallon ta Yy danbe yarda ba yasan da dalilin dayasa take kuka,

anacikin haka ,Fatima taxo. Nemanta ,tasame su tare da sir Aliyu, nan yakalli Fatima yace meyasa take kuka.

Fatima tace dan ba,azo mata visiting ba ,kumafa ba,a mata fashin xuwa duk month ,tayi masa karya.

Nan Fatima ta ce, dama  naga ban gankiba nazo nan muna  hostel kisamemu a can, 

Bata jira amsartaba tayi tafiyarta cike da tausayin kawar tata.

Sir Aliyu yyi gyaran murya yace, dan ba zo miki visiting ba shine kke wanna n kukan.

Ai xasu zo,kobasuzo yauba zasuzo gobe da safe,kiyi shiru kinji kidena kukan haka nan.

Goge hawayen  take wasu na sake zubowa,kallonta yyi fuska atamke yace .

Bazaki dena kukanba ko,wato ni ban isa kiji maganatabako, kinfi son kibatamun rai dankinga nadamu dake ko?

Da sauri ta girgiza kanta hade da hadiye kukan ,tace ,kayi hakuri na bari bazan sakeba.

Har cikin ransa yaji dadin maganar ta ,nan yace share hawayen.

Bamusu ta goge,yace muje ko,kallon sa tayi,yace yes muje, ba musu tabi bayansa har office.

Bayan sun zauna yace ta yi serving in su ,nan tayi  serving a plate daya tatura masa gabansa .

Kallon ta Yy yace to bissimilla,nan suka faraci har suka gama batare da Hafsat ta yadda sun had'a ido da sir Aliyu ba.


Har ransa yaji Dadi daskaci abinci atare ,dan besan daliliba, yanajin  farin ciki duk sadda suke atare ko suke cin abinci.

Bata kallesaba tace yaya natafi ,sai anjima, ji yake kamar yace ta zauna suyi fira.

Amma girman kai yahanasa ,ya furta,dan kada tama yimasa wata fahimta. Kawai sai yace

Ok sai anjima ,nan tafita, tayi hostel dan dama anxoma Fatima  tun dazu.

Washe gari Monday , suna  class after break ,aka turo wata ss1  ana kiran Hafsat Aminu a bakin get.

cikin mamaki Hafsat tabi bayan yarinyar,suna zuwa get me gadi yace gashi inji babanki,

Yana sauri yace abaki, baki bud'e ta kalli uban kwalayen da akace inji babanta da kaya Niki nik'i,

Kallon baba me gadi tayi tace gsky  bani bace k'ila dai watace.

Harararta yyi yace kece mana, dama kwanaki yakawo sak'o abaki kikace wai bake bace ,amma kika karbe.

Dan haka in bakiso ,zaki iya tafiya ,jiki ba lakka ,ta kira wata mate dinsu zata wuce ,

Ta tayata suka kwashe kayan suka kai hostel , tana mamakin kayan.

Koda ta fada ma Fatima,ita wai ji take kamar ba,ita ake nufi ba.

Fatima ,ta nuna mata cewa,itace tason ko babanta yasami budi,Kuma ai bakomai ke tabbata ga dan adamba.

Da haka Fatima ta shawo kan Hafsat ,harta saki ranta.

Koda sir Aliyu yashigo class dinsu yalura Hafsat nackin farin ciki.

Dan haka yyi ta mata tambayoyi ,tana bashi amsa ,da haka har akayi ring in ,dazai fita yace su dage da karatu  dan sauran 1 week exam....

Share pls

Comments

Popular posts from this blog

SIRRIN GANYAN ZOGALE (MORINGA)

CUTAR DA ISTIMNA'I YAKE YIWA ZAKARIN DA NAMI DA LALATA FARJIN MACE TARE DA MAGANIN SA